Da amfani da mitar wutar lantarki na zamani da biyan kudin bil wanne ya fi?

A ganina kati ya fi – Muhammad Sani Amina Abdullahi, Yola Muhammad Sani: “Ni a ganina mita mai amfani da kati ta fi kyau domin kana da iko a kanta. Kati yana karewa za ka je ka saya. Illar amfani da mita shi ne kana zamanka kawai sai su zo su yanke maka wuta. Na katin […]

Da amfani da mitar wutar lantarki na zamani da biyan kudin bil wanne ya fi?
Da amfani da mitar wutar lantarki na zamani da biyan kudin bil wanne ya fi?

A ganina kati ya fi – Muhammad Sani

Amina Abdullahi, Yola

Muhammad Sani: “Ni a ganina mita mai amfani da kati ta fi kyau domin kana da iko a kanta. Kati yana karewa za ka je ka saya. Illar amfani da mita shi ne kana zamanka kawai sai su zo su yanke maka wuta. Na katin kuma ba a yanke wuta domin iya kudinka iya shagalinka.”

Gaskiya ta kati za ta fi – Auwal Adamu

Amina Abdullahi, Yola

Auwal Adamu: “Yadda muka tsinci kanmu a, gaskiya na katin zai fi a kan na mita. Saboda a na mitar, kasar ta zama yadda ta zama. Ba lallai ba ne a zo a karanci mitarka kamar yadda ya kamata. Wani lokaci abin da mita za ta nuna daban kuma abin da za a ba da daban. Misali kamar gida wanda kayan lantarkinsa bai wuce fanka da dan hasken lantarki sai dan firiji daya ba. Amma sai a zo a samu bil na fiye da yadda kake tsammani.”

Wutar mita ta fi – Muhammad Nasir Muhammad

Lubabatu I. Garba, Kano

Muhammad Nasir Muhammad: “Ni ina ganin wutar mita wacce muka saba amfani da ita ta fi, musamman ga masu karamin karfi. Shi wannan katin talaka ba zai iya amfani da shi ba, domin babu kati mai karamin kudi wanda talaka zai iya saye. Sai dai su kamfanonin bayar da wutar su yi gyara yadda za a rika dora wa kowane mutum daidai harajin kudin wutar da ya sha. Sanna su toshe duk wata hanya da ma’aikatansu za su karbi kudi a hannun abokan hulda su ki biyan kamfani. Idan aka yi haka tabbas kowa zai biya kudin wuta a kan lokaci.

Wutar kati ta fi –Usaini Labaran Kankarofi

Lubabatu I. Garba, Kano

Usaini Labaran Kankarofi: “Ni a ganina wutar kati ta fi saboda za ka biya abin da ka yi amfani da shi. Ba cuta ba cutarwa. Idan kana da kudi ka sha wuta idan babu kuma shi ke nan. Amma ita ta mita cutar mutane kamfani ke yi domin idan aka kai wa mutum bil sai ya ki biya ya dan bayar da wani abu daga ciki su kuma ba za su sa a asusun kamfani ba sai dai su dure a aljihunsu. Kamata ya yi kamfanonin samar da wutar lantaki su zuba jari wajen samar da mitocin nan na kati yadda za a sanya a kowane gida, na tabbata kudinsu zai dawo cikin kankanen lokaci, domin zai kasance babu cuwa-cuwa a ciki.”

Sayen kati ya fi dadin sha’ani – Khadijat Isah

John Wada, Lafiya.

Hajiya Khadijat Isah: “Ni dai a nawa ra’ayi wutar lantarki na kati ta fi dadin sha’ani. Domin ka ga na bil a da ne yake da tasiri, amma yanzu sai ka ga ana kawo bil na makudan kudi a karshen wata amma ba a kawo wutar ba. Amma shi na kati kawai abin da ake bukata shi ne katin. Da zarar ka sanya ba za ka fuskanci wata matsala ba sai dai ka ci gaba da amfani da wutar har lokacin da katin ya kare. Saboda haka a ganina wannan na katin da zamani ya kawo mana ya fi wanda aka saba da shi.”

Wutar lantaki ta kati ta fi ta bil – Saraya Agidi

John Wada, Lafiya.

Misis Saraya Agidi: “A gaskiya ba za a ma kwatanta su ba. Don na katin da aka kirkiro da shi din nan tamkar mafita aka kawo wa al’ummar kasar nan da ke fama da matsalar rashin wutar lantarki. Don ni dai koda na katin ya fi tsada, amma idan za a samu a kowane lokaci ya fi wanda ake biya kuma ba a samun wuta. Saboda haka da Gwamnatin Tarayya za ta karfafa ta kuma tallafa wa ire-iren wadannan kamfanoni da an dade da magance matsalar wutar lantarki a kasar nan.”